<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>198</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1)Ku yi ta wa'azi wurin mutane duk,
 Gama a duniya akwai wahalar rai.
 Bari duk Masu Bi su shaida ko'ina,
 Mai Taimako ya zo.

[V2]
 KORUS
 Mai Taimako ya zo, Mai Taimako ya zo,
 Ruhu Mai Tsarki da Allah ya aiko.
 Ku labartad da shi wurin mutane duk,
 Mai Taimako ya zo.

[V3]
 2) Mun sami haskensa, ya watsa duhunmu,
 Ya kau da tsoro duk, ya ba mu kwanciyar rai.
 Ya kawo gafara ta dukan zunubi,
 Mai Taimako ya zo.
 Korus

[V4]
 3) Ga Ubangijinmu, ya zo da warkarwa.
 Ga ƴaƴan duniya, ruɗaɗɗu na Shaiɗan.
 Ya kwance ɗaurarru, ya kawo fansarsu,
 Mai Taimako ya zo.
 Korus

[V5]
 4) Ya Allah mai ƙauna, ko ni na iya ƙi
 In shaida j inƙanka ga dukan mutane?
 Ga ni da, matacce, ka ba ni sabon rai,
 Mai Taimako ya zo.
 Korus</lyrics>
<title>Ku Yi Ta Wa'azi Wurin Mutane Duk LW198</title>
</song>